Duration
00:20:29
Size
18.75 MB
Purchases
5
Category
Adventure
"A duniya mai ban kasa bakwai, Duniyar da mutane ke iya sarrafa Aljanu, sinadarai irinsu Wuta, Iska, ruwa da walkiya, Wani saurayi mai suna Armad Wilbafos yaci Alwashin canza tsarin duniya, inda ya fito neman wani mutum da babu wanda ya taba ganinsa hakanan ba'asan wurin da yake ba gababayan Doron kasashen Duniya. Sun dukufa domin neman wannan mutumi har na karni bayan karni batare da sun sameshi ba. Mutumin yana cikin wata kabilace mai suna BELLIGEES su wayannan kabilar Allah ya Albarkacesu da tsawon rayuwa A duniya, don zasu iya rayuwa har na karni dubu batare da sun mutuba, mutumin ya kirawansa da suna TARIFIL FAKTA. Armad Wilbafos ya rasa mahaifinsa akan wannan dalili, hakananan an kashe yar uwarsa duk akan wannan dalili, zuri'arsa taki karbun faduwa inda mahaifiyarsa itama ta shiga fadan itana daga karshe ya rasata, ya kasance shidayane jal dan zuri'arsu dake numfashi a ban kasa wanda ke da burin cigaba da tafiya akan wannnan tafarki, ahaka ya cigaba da gumurzu inda a kokarinsa na nemo TARIFIL FAKTA ne yai Arangama da wani NAGARTACCEN SIRRI, SIRRIN DA ZAI RIKITA DUNIYA BAKI DAYANTA. Sirrin dake Tattare da kashe masa yar'uwa da mahaifinsa da akai Sirrin dake tattare da kabilar BELLIGEES kabila masu tsawon rayuwa a duniya Sirrin dake Tattare da sarrafa Aljanu da mutane keyi Sirrin dake Tattare da Mutumin da duniya ke nema ruwa a jallo TARIFIL FAKTA Ni karde nee-yi Kishen, Ni karde ne oruka, Ni karde ne kaisaisi, Ni karde tuwa, Ni Karde ne Ururu UBAN GIJIN MASARAUTAR: DAKE SAMAN RANA, UBANGIJIN KAMBU, UBANGIJIN BAN KASA BAKWAI, UBANGIJIN MARA MUTUWA, UBANGIJIN URURU"
The author of "Magajin Wilbafos" is Abdullahi Muhammad (also referred to as Abdullahi Ibrahim Muhammad). He is a Nigerian author known for his work in the fantasy and magical realism genres, with his books being shared on platforms like the "MAGAJIN WILBAFOS _ Littafin Izza" Facebook group.
View more books by Dr Abdullahi1 rating
Masha allah gaskiya wannan tsarin yayi daidai
by Dr Abdullahi
30.00 $AYRID